Erik ten Hag ya ce, bai sani ba ko Jadon Sancho zai ƙara buga wa Manchester United wasa nan gaba.
Mai shekara 23 yana atisaye shi kaɗai ne ba tare da sauran ‘yan wasa ba, bayan da ya yi iƙirarin ɗora masa laifin rashin sanya shi cikin ‘yan wasan da suka buga karawa da Arsenal.
Ten Hag ya sanar cewar dalilin da bai yi amfani da Sancho ba a karawar, saboda ƙwazonsa a atisaye ya ragu.
An tambayi Ten Hag ko zai sake saka ɗan ƙwallon a wasa sai ya ce ”Ban sani ba.”


