Mazauna wasu ƙauyuka a yankin ƙaramar hukumar Gudu ta jihar Sokoto, na ci gaba da tsere wa gidajensu, saboda ƙaruwar hare-haren ‘yan fashin daji.
Wani ya tabbatarwa da BBC cewa, hare-haren ‘yan fashi babu ƙaƙƙautawa a baya-bayan nan, da rashin ɗaukin jami’an tsaro sun tilasta wa mutanen ƙauyen tsallaka iyaka zuwa Jamhuriyar Nijar.
Gwamnatin jihar Sokoto dai ba ta ce komai ba kan wannan al’amari na ƙaruwar hare-haren a yankin na Gudu.