Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) karkashin wata kungiya ta matasa mai suna, Grassroots Governance Group da aka fi sani da APC G3, ta bayar da tabbacin cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, zai jajirce wajen ganin an samu hadin kai da bunkasar tattalin arzikin kasa.
Kungiyar wacce ta bayar da wannan tabbacin a bukin kaddamar da reshen jihar Legas, ta dorawa mambobin kungiyar yakin neman zabe ga ‘yan takarar jam’iyyar a matakin tarayya da jiha.
A Legas, kodinetan APC G3 na kasa, Amechi Chuks. Oyema, ya yi kira ga mambobin kungiyar goyon bayan da su tabbatar an kai sakon tikitin takarar shugaban kasa na Tinubu/Shettima zuwa ga talakawa.
Ya ci gaba da cewa, Tinubu na da abin da ake bukata domin hada kan Najeriya da bunkasa tattalin arziki.
Onyema ya bayyana cewa, Kungiyar Tallafawa masu tsattsauran ra’ayi a jihohi 36 da kuma babban birnin tarayya Abuja sun shirya tsaf don baiwa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC kuri’u tsakanin 300,000 zuwa 500,000.


