Cristiano Ronaldo ya ce, Manchester United ta ci amanar sa yayin da ya ce, mai horas da kungiyar Erik ten Hag da wasu manyan jami’an gudanarwa na kokarin tilasta masa ficewa daga kungiyar a wata hira da aka yi da shi ranar Lahadi.
Dan wasan wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or sau biyar, ya kasance dan wasa a fili a United tun lokacin da Ten Hag ya karbi ragamar horar da ‘yan wasan a watan Mayu.
An ladabtar da Ronaldo ne bayan da ya ki zuwa maye gurbinsa a wasan da suka doke Tottenham da ci 2-0 a watan da ya gabata, amma ya koma taka leda a ‘yan makonnin nan, har ma ya zama kyaftin dinkungiyar a wasan da Aston Villa ta doke su da ci 3-1 a karshen makon jiya.
Ronaldo ya koma Old Trafford a watan Agustan 2021 daga Juventus.
Zamansa na farko a United ya kasance mai daukaka a karkashin jagorancin Alex Ferguson, inda ya lashe kofunan Premier uku, gasar zakarun Turai da kuma na farko na lashe kyautar Ballon d’Or a matsayin dan wasa mafi kyau a duniya.
Duk da kwallaye 24 da ya ci a duk wasannin da ya buga a kakar wasan da ta wuce, United ta sha fama da mummunan kamfen yayin da ta kare a matsayi na shida a gasar Premier kuma ta kasa tsallakewa zuwa gasar zakarun Turai.