fidelitybank

Tashin Fubara da suka koma APP sun lashe zaɓen ƙananan hukumomin Rivers

Date:

Jam’iyyar Action People’s Party (APP) ta lashe zaɓen shugabannin ƙananan hukumomi 22 cikin 23 na jihar Rivers da aka gudanar ranar Asabar.

Shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta na jihar (RSIEC), Adolphus Enebeli ne ya bayyana sakamakon ranar Asabar da daddare a Fatakwal, babban birnin jihar.

Haka kuma, hukumar zaɓen ta dakatar da bayyana sakamakon zaɓen ƙaramar hukumar Etche, saboda a cewarta har lokacin ana ci gaba da tattara sakamakon zaɓen ƙaramar hukumar.

Shugaban na RSIEC ya kuma ce za a bayyana sakamakon zaɓen kansilolin duka mazaɓun jihar 319 tare da na shugaban ƙaramar hukumar Etche da zarar an kammala tattara sakamakon.

Tun da farko dai jam’iyyar PDP mai mulkin jihar ta ce ba za ta shiga zaɓen ba, sakamakon umarnin wata kotu da ta hana gudanar da zaɓen, kodayake gabanin zaɓen uwar jam’iyyar ta ƙasa ta yi kira ga ‘yan jam’iyyar su shiga zaɓukan.

Gwamnan jihar Siminalayi Fubara na takun-saƙa da tsohon gwamnan jihar, ministan Abuja Nyesom Wike, kan jagoirancin jam’iyyar PDP a jihar.

Rikicin na su ya yi ƙamari ne lokacin da aka gudanar da zaɓen shugabannin jam’iyyar jihar, bayan da tsagin Wike ya samu nasara kan tsagin Fubara, lamarin da ya sa magoya bayan Fubara suka fice daga PDP zuwa APP, inda suka yi takarar a can, shi kuwa Gwamna Fubara ya goyi bayansu.

Abin da masu sharhi ke kallon wani mataki ne na ficewar Fubara daga PDP, kodayake bai fitar da wata sanarwa a hukumance ta aniyar ficewa daga jam’iyyar ba.

breaking news in nigeria today 2021

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Kare Ya Kashe Ragon Layya: Mai ƙwacen waya ya kashe Sojin ruwa a Kaduna

Wani mai ƙwacen waya ya kashe wani soja bayan...

Sojoji sun hallaka ƴan Boko Haram da dama

Da sanyin safiyar ranar Litinin, dakarun rundunar Haɗin kai...

Tarzomar kama baƙin haure a Amurka na yamutsa hazo

An shiga rana ta uku a tarzomar da ake...

Alhazai sun kammala aikin Hajji bana

A ranar Lahadin da ta gabata ne alhazai miliyan...

Tinubu gyaran ƙasa za ka mayar da kai ba zaɓen 2027 ba – ACF

Ƙungiyar Tuntuɓar Juna ta Arewacin Najeriya, ta yi kira...

Ƴan Jagaliya sun caka wa Matashi kuwa lokacin da ya zo karɓar naman Sallah a Kano

Matashi Ibrahim Mahmud ya rasu sakamakon caka masa wuƙa...

Kallo Ya Koma Sama: Elon Musk zai fuskanci mummunar sakamako – Trump

Ana ci gaba da takun saka tsakanin shugaban Amurka...

Zulum ya miƙa kyautar Naira miliyan 100 ga iyalan Sojojin da aka kashe

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya bai...

Otal ɗin ƴan Najeriya ya kama da wuta wani ɓangaren a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce an samu tashin...

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...
X whatsapp