Masarautar Daura a jihar Katsina, ta sanar da ranar da za ta yi bikin nadin sarautar, Yusuf Buhari a matsayin Talban Daura.
Yusuf Buhari da ga shugaba Muhammadu Buhari wanda a ka yi masa aure a kwanakin baya, wanda ya auri ‘yar gidan Sarkin Bichi, Nasiru Ado Bayero a jihar Kano.
Masarautar dai ta fitar da sanarwar ne a ranar Lahadi, wadda ta bayyana cewa, za a yi bikin nadin sarautar ne a ranar 18 ga watan Disamba a fadar mai martaba Sarkin Daura.