fidelitybank

Siyasa: Sanata ya raba motoci 50 da Babura 500 da firji 600

Date:

Sanata mai wakiltar Gombe ta Arewa a majalisar wakilai ta kasa, Sa’idu Alkali, ya raba kayan tallafi na miliyoyin Naira ga mazabar sa.

Kayayyakin da a ka raba sun hada da motoci 50, babura 500, injin dinki da firij 600, famfunan hannu na noman rani, masuskar shinkafa da sarrafa masara ga manoma 1,000 da dai sauransu, a Gombe ranar Lahadi.

Da ya ke jawabi a wajen bikin rabon kayayyakin, Sanatan ya ce, “Hakan shi ne nasa hanyar nuna jin dadi na ga al’ummar mazaba ta na ganin na cancanci wakilce su a karo na Uku a majalisar dattawa”.

Ya ce kuma ce”A cikin ayyukan mazabarsa na 2021, na gina tubalan ajujuwa da cibiyoyin kiwon lafiya, na samar da ayyukan ruwa da hanyoyin mota a fadin kananan hukumomin guda biyar da na ke wakilta, Dukku da Gombe da Kwami da Funakaye da kuma Nafada”. Inji Sanata.

A nasa jawabin, Gwamna Inuwa Yahaya ya yabawa Sanatan bisa yadda ya baiwa al’ummar mazabar sa kwarin gwiwa, sannan ya bayyana fatansa na ganin cewa abubuwan karfafawa za su yi tasiri ga rayuwar al’ummar mazabar sa.

the nation news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Mun ceto tsohuwa ƴar shekaru 80 daga masu garkuwa – Ƴansanda

Rundunar ƴansandan jihar Jigawa, ta ce ta ceto wata...

APC na taron kasu ruwa da tsaki

Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya za ta gudanar da...

Matatar Ɗangote ta sake karya farashin fetur

Kamfanin Dangote da ya mallaki matatar mai ta Dangote...

Idan Isra’ila ta kai mana hari Amurka ce – Iran

Ministan harkokin wajen ƙasar Iran ya ce, gwamnatin Tehran...

Kotu ta daure mai kiwon Akuya bayan ta cinye shukokin gwamnatin Kano

Wata kotun majistare da ke Kano ta daure wasu...

‘Yansanda sun dakile yi garkuwa da mutane a Katsina

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta dakile wani yunkurin...

‘Yansanda sun dakume ‘Yan Fashi uku a Kano

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wasu ‘yan...

Jarumar Nollywood ta zama sojan ruwar Amurka

Fitacciyar jarumar nan ta Najeriya Grace Bassey wacce a...

Na yi takaicin barin Ancelloti daga Real Madrid – Carvajal

Dan wasan baya na kungiyar kwallon kafa ta Real...

Mu na shirin yin kawancen jam’iyya – PDP

Majalisar dattawa ta jam'iyyar PDP, ta bayyana shirin jam'iyyar...

Ana zanga-zanga a Binuwai sakamakon harbe Dalibi dan shekara 23

Wata zanga-zanga ta barke a Makurdi, babban birnin jihar...

A na cigaba da farautar Fursunonin Osun da suka tsere

Hukumar gyaran hali ta Najeriya (NCoS) ta ce, ta...
X whatsapp