Shugaban karamar hukumar Akwanga a jihar Nasarawa, Emmanuel Leweh ya rasu.
Sahara Repoters ta rawaito cewa, Laweh ya fadi ya mutu a wani asibiti mai zaman kansa da ke Abuja babban birnin Najeriya ranar Alhamis.
Wani dan uwa kuma dan majalisa a majalisar dokokin jihar, Samuel Tsebe, ya ce, marigayin ya ga na da ‘yan majalisarsa a ranar Litinin kafin lamarin ya faru.
An dai bayyana cewa Leweh ya shafe watanni uku ya na mulki a matsayin shugaban majalisar.
Tsebe, wanda ya tabbatar da mutuwar, ya ce, Leweh ya rasu ne bayan gajeriyar rashin lafiya.