fidelitybank

Sarkin Daura ya naɗa Yusuf Buhari a matsayin Talban Daura, shekaru 2 bayan ya baiwa Alpha Conde sarautar

Date:

Sarkin Daura, Umar Faruk Umar ya naɗa Yusuf Buhari, ɗan gidan Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a matsayin Talban Daura.
A watan Agusta na shekarar 2019, Sarkin Daura ya naɗa Shugaban Kasar Gini na wannan lokacin, Alpha Conde a matsayin Talban Daura.
Bayan ya naɗawa Conde rawanin Talban Daura, Sarkin ya kuma kyautar doki, takobi da shanu, inda ya ce ya cancanci tagomashin sakamakon kaunar da ya ke yinwa Buhari.
Duk da cewa har yanzu Shugaban Kasar Gini ɗin ne mai riƙe da sarautar, a watan Satumbar nan kuma sai Sarkin ya sanar da cewa ya naɗa Yusuf Buhari a matsayin Talban Daura.
A jiya Asabar ne a ka yi gagarumin bikin naɗin sarautar a fadar Sarkin Daura.
A wajen bikin, Sarkin ya baiyana cewa an naɗa Yusuf Buhari a matsayin Talban Daura kuma Hakimin Kwasarawa sakamakon irin ci gaban da mahaifinsa ya kawowa garin Daura.
Ya yi bayanin cewa ɗan gidan Shugaban Kasar zai rika zuwa masarautar Daura a -kai -a- kai domin bada gudunmawar sa a wajen ci gaban garin.
Waɗanda su ka halarci bikin sun haɗa da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osibanjo, Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmed Lawan da Shugaban Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila.
Sauran sun haɗa da Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje da takwaransa na Katsina, Aminu Masari da sauran manyan baƙi.

legit nigeria news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Za mu ɗauki matakin hana sake faruwar kisan mutane – Gwamnatin Filato

Gwamnatin jihar Filato ta jaddada aniyarta ta ɗaukar mataki...

Babu barazanar tsaro a Abuja – Najeriya

Gwamnatin Tarayya ta ce, babu wata barazanar a babban...

Isra’ila za ta mayarwa da Iran martani duk da tsagaita wuta

Ministan tsaron Isra'ila, Katz ya bayyana cewa, ya ba...

Ba mu kai wa Isra’ila hari ba – Iran

Kafar watsa labarai ta Iran ta ruwaito gwamnatin ƙasar...

Duk da faduwar farashin mai NNPCL ya kara farashi

Kamfanin man fetur na Najeriya, NNPCL ya ƙara farashin...

Duk wasu ƙawayen Amurka za su ɗanɗanar kuɗarsu – Iran

Rundunar dakarun juyin juya halin Iran ta fitar da...

Iran ta mayar da martani kan sojojin Amurka dake Qatar

Kafofin yaɗa labaran Iran sun bayyana cewa ƙasar ta...

Faransa ba ta goyon bayan Amurka na kifer da gwamnatin Iran – Barrot

Ministan harkokin wajen Faransa ya ce, ƙasarsu ba ta...

Kotu a Kano ta ɗaure masu satar Yara

Babbar kotun jihar Kano da ke zamanta a Miller...

Ba wata hujja da Amurka za ta kai wa Iran hari – Rasha

An gudanar da tattaunawa tsakanin shugaban Rasha Vladimir Putin...

Tinubu ya miƙa saƙon ta’aziyya ga mutanen Kano da Kaduna da Borno

Shugaba Bola Tinubu ya yi Alla-wadai da kisan wasu...

Amurka ta tafka babban kuskure – Iran

Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya yi Alla-wadai...
X whatsapp