Hukumar ƴan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ta ce sama da mutum 100,000 ne suka yi hijira daga Lebanon zuwa Syria tun bayan ƙazancewar yaƙin Isra’ila da Hezbollah a makon da ya gabata.
Hukumar ta ce yawancin mutanen ƴan asalin ƙasar Syriyar ne wadanda suka guje wa yaƙin basasa a ƙasarsu.
Shugaban hukumar, Filippo Grandi ,ya ce adadin mutanen da ke gudun hijirar ya ninka cikin kwana biyu.
Firaministan Lebanon Najib Miƙati ya ce mutane kusan miliyan ne yaƙin ya raba da muhallansu a Lebanon.


