Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya ce, dole sojoji su fatattaki ƴanbindiga su ƙwace dazukan Najeriya domin kawo ƙarshen rashin tsaro.
Ganduje ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai ta’aziyar jaje ga Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umar Bago bisa rasuwar gomman mutane a sanadiyar gobarar fashewar tanka a jihar, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
A wata sanarwa da sakataren watsa labaran jam’iyyar APC na ƙasa, Edwin Olofu ya fitar a ranar Alhamis a Abuja, Ganduje ya ce akwai buƙatar a ƙara ƙaimi, musamman wajen fatattakar ƴanbindiga daga dazukan Najeriya domin kawo ƙarshen yaƙin harkokin ƴanbindiga a ƙasar.
“Hanyar da za a magance wannan matsalar ita ce a ƙwace dazuka saboda ƴanbindigar nan a cikin dazuka suke zama. Me ya sa muka koma muna jira su kawo hari, kafin mu tare su? lokacin da nake gwamna, kira na yi ga gwamnatin tarayya da ta zuba sojoji a dajin Falgore, wanda hakan ya sa aka kafa sansanin horar da sojoji.
“Tun daga lokacin ne aka fatattaki ƴanbindiga daga dajin, kuma Kano ta samu zaman lafiya,” in ji Ganduje.
Da yake mayar da martani, Gwamna Bago ya yi godiya bisa ziyarar jajen, sannan ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta gyare titin Suleja-Minna domin rage yawaitar haɗura.