Sabuwar firaministar Birtaniya Liz Truss, ta gana da Sarauniya a fadarta da ke Balmoral Castle a wani bangare na shirye-shiryen rantsar da ita a matsayin firaministar kasar ta gaba.
Wannan na zuwa ne bayan da a safiyar yau firaminstan mai barin gado Boris Johnson ya gana da Sarauniyar in da ya mika takardar murabus dinsa.
Sarauniyar ta yi fama da matsalar tafiya, wannan ne ma dalilin da ya sa aka yi ganawar a fadarta ta Balmoral Castle da ke Scotland, a maimakon fadar Buckingham da ke Landan. In ji BBC.


