Kyaftin din Al-Nassr, Cristiano Ronaldo ya bukaci kungiyarsa da ta sayi dan wasan baya, Pepe, mai shekaru 40, daga FC Porto, a cewar kwararre kan harkokin kwallon kafar Portugal, Pedro Almeida.
Almeida ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter.
Ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa, “Cristiano Ronaldo ya nemi hukumar Al-Nassr ta sa hannu #Pepe, dan wasan Portugal din yana karshen kwantiraginsa da Porto.
“Porto na son tsawaita kwantiragin da dan wasan.”
Ronaldo da Pepe tsoffin abokan wasan kungiyar ne a lokacin da suke Real Madrid.
Ronaldo ya koma Al-Nassr a kyauta bayan ya bar Manchester United bisa amincewar juna a watan Nuwamban bara.


