Sojojin Najeriya sun hallaka wasu riƙaƙun ƴan fashin daji biyu da su ka addabi jihar Zamfara da maƙwabtatanta da su ka haɗar da Kachalla Ruga da kuma Alhaji Auta.
Jaridar PrNigeria ta rawaito cewa, mutanen biyu sun gamu da ajalinsu ne yayin luguden wutar jiragen sojin saman Najeriya, a wasu dazuka da ke ƙauyen Gusami da kuma kauyen Tsamre a karamar hukumar Birnin Magaji.
Kafin mutuwarsu dai su na cikin gawurtattun ƴan fashin dajin da su ka addabi Arewa maso yammacin Najeriya.
Wasu majiyoyi sun ce an kuma hallaka yaransu da dama a lokacin hare-haren.