fidelitybank

Ramuwar Gayya: Bururruka sun kashe Karnuka 250

Date:

Wasu tarin Bururruka a wani birnin Indiya sun kashe karnuka 250, tare da jefo su daga saman manyan gine-gine da bishiyoyi.

Kafar labarai ta News18 ta rawaito cewa, mazauna yankin Labool, wani gari ne mai kimanin mutum 5,000 da ke da nisan mil 300 a Gabas da birnin Mumbai, sun shaida wa News18 cewa, Birrai sun fara daukar fansa ne a watan jiya bayan da wasu karnuka su ka kashe wani dan biri.

Mazauna yankin sun ce tun daga lokacin ne birrai su ka fara farautar karnuka ta yadda da zarar sun hango su sai su ja su zuwa saman dogayen gine-gine ko bishiyoyin suna jefo su kasa har lahira.

Kafar labarai ta Newsweek ta rawaito cewa, kusan kowane Kare a garin an kashe shi.

Newsweek ta ce, an kira jami’ai daga Sashen Kula da Dazuzzuka a yankin, domin su taimaka wajen kama Birran, amma ba su iya kama ko daya ba. Daga nan ne mazauna kauyukan su ka yi kokarin kama su.

News18, ta ce, da yawa daga cikin Birran sun samu raunuka a kokarin kisan karnukan.

“Birrai a yanzu suna kai hari kan kananan karnuka, suna haifar da ‘firgici’ a yankin Labool,” kamar yadda News 18 ta rawaito.

Mataimakin Farfesa a Jami’ar SUNY Buffalo, Stephanie Poindedter, wanda bincikensa ya mayar da hankali a kan halayyar halittu wadanda suke da tafin hannu, tafin kafa da kuma fuska mai dauke da idanu da suke fuska kamar dan Adam da birrai, ya ce, “A cikin binciken da aka yi game da irin wadannan halittu da ake killacewa, a cikin wuraren da jama’a ke ziyarta kamar gidajen namun daji, mun gano cewa lokacin da aka kai wa irin halittun hari ta wata hanya, akwai yiwuwar su mai da martani ta hanyar kai hari ga wanda ke da alaka da wanda ya zalunce su, kuma martanin zai fi tsanani fiye da yadda aka kai masu”. A cewar Dailytrust.

 

legitnewsnigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Za mu ɗauki matakin hana sake faruwar kisan mutane – Gwamnatin Filato

Gwamnatin jihar Filato ta jaddada aniyarta ta ɗaukar mataki...

Babu barazanar tsaro a Abuja – Najeriya

Gwamnatin Tarayya ta ce, babu wata barazanar a babban...

Isra’ila za ta mayarwa da Iran martani duk da tsagaita wuta

Ministan tsaron Isra'ila, Katz ya bayyana cewa, ya ba...

Ba mu kai wa Isra’ila hari ba – Iran

Kafar watsa labarai ta Iran ta ruwaito gwamnatin ƙasar...

Duk da faduwar farashin mai NNPCL ya kara farashi

Kamfanin man fetur na Najeriya, NNPCL ya ƙara farashin...

Duk wasu ƙawayen Amurka za su ɗanɗanar kuɗarsu – Iran

Rundunar dakarun juyin juya halin Iran ta fitar da...

Iran ta mayar da martani kan sojojin Amurka dake Qatar

Kafofin yaɗa labaran Iran sun bayyana cewa ƙasar ta...

Faransa ba ta goyon bayan Amurka na kifer da gwamnatin Iran – Barrot

Ministan harkokin wajen Faransa ya ce, ƙasarsu ba ta...

Kotu a Kano ta ɗaure masu satar Yara

Babbar kotun jihar Kano da ke zamanta a Miller...

Ba wata hujja da Amurka za ta kai wa Iran hari – Rasha

An gudanar da tattaunawa tsakanin shugaban Rasha Vladimir Putin...

Tinubu ya miƙa saƙon ta’aziyya ga mutanen Kano da Kaduna da Borno

Shugaba Bola Tinubu ya yi Alla-wadai da kisan wasu...

Amurka ta tafka babban kuskure – Iran

Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya yi Alla-wadai...
X whatsapp