Mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo, ya mika sakon ta’aziyyar Sarauniya a madadin ‘yan Najeriya.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Tuwita Osinbajo ya ce, ”Najeriya ta bi sahun gwamnati da al’umar Birtnaiya, da kungiyar Kasashe Rainon Ingila ta Commonwealth da kuma sauran al’umar duniya wajen mika sakon ta’aziyyarsu ga masarautar Birtaniya game da rasuwar Sarauniya Elizabeth II”.
Sauran shugabanni na cigaba da miƙa saƙon ta’azziyyar su ga Birtaniya, bisa mutuwar ta Sarauniya.


