Jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) reshen Jihar Kaduna ta maka Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) Kotu.
Tana neman a soke Sanata Uba Sani dan takarar gwamna na jam’iyyar APC bisa zargin tafka magudi a zaben fidda gwani da aka gudanar a ranar 27 ga watan Mayun 2022.
Lokacin da aka gabatar da karar a gaban mai shari’a Hadiza R. Shagari ta babbar kotun tarayya da ke Kaduna a ranar Juma’a, dukkanin bangarorin sun nemi a kara musu lokaci domin su shirya su kuma mayar da martani ga bukatar.
Kungiyar lauyoyin NNPP ta samu jagorancin Mista Wole Agunbiade (SAN). APC tana da Barista Sule Shuaibu, yayin da lauyar INEC Barista Halima Gachi.
Don haka mai shari’a Shagari ya dage sauraron karar zuwa ranar 15 ga watan Satumba, 2022 domin sauraren karar.
Yayin da yake zantawa da manema labarai ta bakin wani dan kungiyar lauyoyin sa jim kadan bayan zaman kotun, Wole Agunbiade ya bayyana cewa suna son tabbatar da cewa hukumar zabe ta INEC ta yi abin da ya dace.
Ya ce bai kamata INEC ta wallafa sunan dan takarar ba saboda APC ba ta gudanar da sahihin zaben fidda gwani ba.
Ya jaddada cewa, “NNPP na kalubalantar zaben fidda gwani na jam’iyyar APC da aka gudanar a ranar 27 ga Mayu, 2022.”
An ayyana Sanata Uba Sani ne a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwani na gwamna na jam’iyyar APC.
Ya samu kuri’u 1,149 ya zama wanda ya yi nasara, yayin da tsohon Mataimakin Kwanturola-Janar na Hukumar Kwastam, Bashir Abubakar ya samu kuri’u 37. Alhaji Mahmood Sani Shaaban ya samu kuri’u 10.


