fidelitybank

Nnamdi Kanu ya sake shigar da kara a kan cimmaka da lafiyar sa

Date:

Shugaban masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu ya sake shigar da sabuwar kara ga babban Lauyan gwamnatin tarayya (AGF) da ministan shari’a Abubakar Malami (SAN) da kuma hukumar tsaro ta farin kaya (DSS).

A halin yanzu dai shugaban mai fafutukar kafa kasar Biafra ya na fuskantar shari’a kan ta’addanci da kuma cin amanar kasa.

A karar da ya shigar a ranar Litinin, Kanu na neman umarnin babbar kotun tarayya da ke Abuja ta tilastawa ‘yan sandan sirrin Najeriya, DSS da su ba shi damar samun abinci, kula da lafiya da canza tufafi kamar yadda mai shari’a Binta Nyako ta bayar a baya.

Lauyan sa Barista Maxwell Chibuike Okpara ne ya shigar da karar mai lamba FHC/ABJ/CS1585/2021 a madadin shugaban kungiyar ta IPOB.

Kanu ya kuma nemi a ba shi umarnin tilastawa hukumar DSS ta ba shi damar shirya abincinsa, wanda a shirye ya ke ya biya.

Har ya zuwa yanzu dai, ba a sanya ranar da za a saurari karar ba.

Mai shari’a Nyako a ranar 2 ga watan Disamba ya umarci hukumar DSS da ta baiwa Kanu damar gudanar da addininsa cikin walwala da jin dadin zaman gidan ajiya da gyaran hali.

vgn news today 2021

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Makami mai Linzami ya faɗa kan cibiyar tattara bayanan sirrin Isra’ila

Kafar yaɗa labarai ta gwamnatin Iran ta ce, ƙasar...

Iran ta ƙaddamar da sabbin hare-haren makamai masu linzami kan Isra’ila

Rundunar sojin Isra'ila ta ce, Iran ta ƙaddamar da...

Isra’ila ta na da makaman nukiliya 90

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya dade yana cewa Iran...

Kashe jagoran Iran Ayatullah shi ne kawo ƙarshen rikici – Isra’ila

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce duk wani shiri...

Jerin sunayen masu Fashin Waya 51 da aka kama a Kano

Rundunar ƴansandan Kano, ta fitar da jerin sunayen Mutane...

Iran ta dakatar da tashin jirgi a ƙasarta

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Iran ta...

Poland za ta kwashe dukkannin ƴan ƙasarta daga Isra’ila

Poland na shirin kwashe kusan ‘yan kasarta 200 daga...

Kisan Binuwai abun haushi ne bai kamata a ƙyale ba – Atiku

Atiku Abubakar ya yi Allah-wadai da Kisan Benue, tare...

Ƴan Bindiga sun ajiye makamai a Katsina

Wasu fitattun jagororin ƴanbindiga da suka addabi yankunan ƙaramar...

Iran ta rataye Mutumin da ya yi mata leƙen asiri

Iran ta ce ta aiwatar da hukuncin kisa ga...

Isra’ila ta ci gaba da neman Mutanen da suka maƙale

Tawagar masu aikin ceto a Isra'ila na ci gaba...

Kotu ta bayar da umarni a kashe Matashi ɗan shekara 23 a Kano

Babbar kotun jihar Kano mai lamba 23 ƙarƙashin mai...
X whatsapp