Hukumar kwallon kafa ta Afrika Caf ta yi watsi da rade-radin da ake ta yadawa na cewa za a iya dauke gasar cin kofin nahiyar Afirka da za a yi a watan gobe daga kasar Kamaru zuwa wata kasar, sakamakon gano sabon nau’in Omicron na Covid-19.
Sabuwar nau’in cutar ya sa wasu kasashe suka bullo da dokar hana zirga-zirga ga kasashen Afirka da dama, tare da Najeriya, makwabciyarta Kamaru, wadda ita ce ta baya-bayan nan da aka saka a cikin kasashen da ba za su shiga Burtaniya.
A cikin ‘yan kwanakin nan, wasu kafafen yada labarai sun ba da shawarar cewa za a canza ranakun gasar na kasashe 24, ko watakila a mayar da gasar zuwa zuwa Qatar.
Daraktan yada labarai na CAF, Alex Siewe, ya ce babu wannan zantukan da a ke ta yadawa.