Kafofin labaran Czech sun bayyana cewa, Najeriya ta soke ziyarar da firaministanta Petr Fiala ya shirya kai wa Abuja, babban birnin ƙasar ta Afirka ta Yamma.
Kakakin gwamnatin Jamhuriyar Czech Václav Smolka ya shaida wa jaridar Blesk ta Czech cewa, “Najeriya ta sanar da mu cewa ba ta iya samar da isashen shirin tarba da tsare-tsaren ziyarar firaminstan ba, don haka mun amince da soke ziyarar.”
Yayin da Najeriya ba ta ce uffan kan lamarin ba, wasu majiyoyin yaɗa labarai na kasar Czech sun nuna cewa wataƙila sokewar na da nasaba da goyon bayan da Czech ke baiwa Isra’ila a rikicin da ake fama da shi da kungiyar Hamas.
Czech dai tana cikin ƙasashen da suka kaɗa ƙuri’ar ƙin amincewa da ƙudurin Majalisar Dinkin Duniya na tsagaita buɗe wuta a rikicin Isra’ila da Hamas, yayin da kuma Najeriya ta amince da tsagaita buɗe wuta.
Fiala ya kai ziyara a yankin kudu da hamadar sahara daga makon da ya gabata don neman damar kasuwanci ga kamfanonin Czech.
Ya zagaya ƙasashen Habasha da Kenya, inda ya tattauna da shugabannin kasashen.
Ana sa ran zai gana da shugaban Ghana Nana Akufo-Addo a Accra a ranar Alhamis, kafin ya kammala ziyarar tasa a Ivory Coast a ranar Asabar.


