fidelitybank

Najeriya na cikin ƙasashen da ake fataucin ‘yan mata zuwa wasu sassan Afirka da Turai – NAPTIP

Date:

Yayin da ake gangamin yaƙi da fataucin ɗan’adam na duniya a yau Talata, hukumar yaƙi da fataucin a Najeriya ta ce masu safarar mutane na amfani da nacewar da ‘yan ƙasar ke yi na sai sun fita ƙasashen waje neman rayuwa mai daɗi suna saka su a ƙangin bauta ta zamani.

Hukumar Naptip ta bayyana cewa tana yaƙi da wannan matsala ta hanyoyi da dama, ciki har da shirya tarukan wayar da kai da kuma aiki da hukumomin tsaro da ‘yan ƙungiyoyi a sassan ƙasar.

Rahotanni sun ambato shugabar hukumar, Farfesa Fatima Waziri-Azi tana shawartar matasa da kada su bari a yaudare su da cewa “idan suka fita ƙasashen waje za su samu rayuwa mai kyau”.

Bayanai na cewa sama da ƴan Najeriya 50 da aka yi safarar su akasari mata da ƴan mata ne aka mayar da su ƙasar daga Ghana a baya-bayan nan.

Wani rahoton ofishin yaƙi da miyagun ƙwayoyi da muggan laifuka na Majalisar Ɗinkin Duniya ya nuna cewa yara sun fi manya fuskantar cin zarafi yayin da ake fataucinsu.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana cewa a duniya baki ɗaya, cikin mutum uku da aka yi safararsu ɗaya daga ciki yaro ne, kuma akasari yara mata ne.

An ware duk ranar 30 ga watan Yulin kowacce shekara don faɗakar da jama’a matsalar da ke tattare da fataucin bil-adama.

Najeriya na cikin ƙasashen da ake fataucin ‘yan mata zuwa wasu sassan Afirka da Turai, inda ake kwaɗaita masu samun rayuwa mai kyau a ƙarshe kuma su faɗa cikin wahala.

Kwamared Hafizu Sanka shi ne jagora ne a ƙungiyar kare haƙƙin ɗan’adam ta duniya ofishin jihar Kano, ya shaida wa BBC cewa safarar mutane abu ne da ke ƙaruwa.

Kwamared Sanka ya ce daga bayanan da suka samu, mutanen da suke zuwa ƙasashen Larabawa adadinsu na ƙaruwa duk da wahalar da suke sha fiye da waɗanda suke zuwa ƙasashen Turai.

breaking news in nigeria today 2021

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp