Najeriya da Poland a ranar Talata a Abuja, sun rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna kan harkokin noma (MOU), inda kasar ta Turai ita ma ta yi alkawarin fadada fannin hadin gwiwar tattalin arziki a bangaren makamashi da masana’antu.
An sanya hannu kan yarjejeniyar ne a lokacin ziyarar shugaban kasar Poland Andrezej Duda, wanda shi ne na farko da wani shugaban kasar Poland ya kai Najeriya, tun bayan kulla huldar jakadanci tsakanin kasashen biyu a shekarar 1961.
Da yake jawabi ga manema labarai tare da shugaban kasar mai ziyara, shugaba Buhari ya ce, Najeriya ta gamsu da hadin gwiwar da ake yi da kasar Poland a fannonin ruwa, ilimi da tsaro.
Dangane da harkokin noma, wanda daya ne daga cikin abubuwan da gwamnatin Najeriya ta sa gaba, shugaban kasar ya ce hadin gwiwa a wannan fanni zai zama nasara ga kasashen biyu, musamman ma a halin da ake ciki na karancin abinci a duniya da ake samu sakamakon rikicin Ukraine.
Ya yi nuni da cewa, daga cikin dimbin kalubalen da duniya ke fuskanta, Najeriya na son samar da sabbin hanyoyin yin hadin gwiwa da suka hada da tattaunawa kan dabaru akai-akai da tuntubar juna ta fuskar siyasa, ba wai kawai dangantakar dake tsakanin kasashen biyu ba, har ma da magance batutuwan da suka shafi shiyya-shiyya da na kasa da kasa.


