fidelitybank

Nadin Yusuf Buhari: Shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan ya isa Katsina

Date:

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya isa jihar Katsina, a safiyar ranar Asabar, domin halartar bikin nadin sarautar Yusuf dan shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari ne ya tarbe shi a filin jirgin Umaru Musa Yar’adua da ke Katsina.

Sarkin Daura, Alhaji Umar Farouk, zai nada Yusuf rawani a matsayin Talban Daura, wanda zai zama Hakimin Kwasarawa.

An shirya gudanar da taron ne a Daura, mahaifar shugaba Buhari.

A tare da Shugaban Majalisar Dattawa daga Abuja akwai Sanata Yusuf Abubakar Yusuf da Mohammed Sani Musa da kuma Bello Mandiya.

A na sa ran shugaban majalisar dattawan ya dawo Abuja nan take bayan kammala taron.

A lokacin da ya nada sabbin hakimai guda hudu a ranar Alhamis, Sarkin Daura ya ce, sun yanke shawarar yi wa dan Buhari rawani ne domin hana sabon Talba yawo daga Abuja da Yola, mahaifar mahaifiyarsa, lokacin da wa’adin shugaban ya kare.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari tar da mai dakin sa, Aisha Buhari na kasar Turkiyya, domin halartar wasu ayyuka.

legitnews.ng

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Dangote ya rage farashin litar mai zuwa ₦820

Kamfanin matatar man Dangote ya rage farashin litar mai...

Dubai ta sake tsaurara matakan bai wa ‘yan Najeriya biza

HaÉ—aÉ—É—iyar Daular Larabawa, UAE ta sake sanya wasu dokoki...

‘Yan Bindigar Katsina ‘yan asalin jihar mu ne – Gwamna

Gwamnan Katsina Umaru Dikko Radda ya ce galibin 'yan...

Zan yi wa ADC aiki ina cikin jam’iyyar PDP – Sule Lamido

Jigo a babbar jam’iyyar hamayya ta PDP a Najeriya...

Buhari da Tinubu kan su a hade ya ke – Garba Shehu

Mai magana da yawun tsohon Shugaban kasa, Muhammadu Buhari...

Ganduje ya kama aiki a hukumar kula da filayen jirgin sama

Tsohon shugaban jam'iyyar APC mai mulki, Abdullahi Ganduje, ya...

JAMB ta amince da maki 150 mafi Æ™anÆ™anta don samun gurbin karatu a jami’o’i

Hukumar shirya jarrabawar shiga Jami'o'i ta Najeriya (JAMB) ta...

ASUU ta dakatar da yajin aikin da ta fara

Ƙungiyar Malaman Jami'o'i ta Najeriya, ASUU da dakatar yajin...

Masu haÉ—akar ADC na É“aÉ“atu ne saboda rashin gwamnati – Radda

Gwamnan jihar Katsina, Mallam Dikko Umar Radda ya yi...

Ba ruwan Biri da gada a makamin Nukiliya – Shettima

Mataimakin shugaba Najeriya Kashim Shettima ya ce ƙasar za...

An kashe Mutane 70 a jihar Filato

Rahotonni daga jihar Filato na cewa Æ´anbindiga sun kai...

Ambaliya ta kashe mutane 100 a Amurka

Hukumomi a jihar Tesxas da ke Amurka sun bayyana...
X whatsapp