Kyaftin din Super Eagles, Ahmed Musa, ya yi karin haske kan jita-jitar da ake yadawa cewa ya fice daga buga wasan kasa da kasa.
Musa dai bai buga wasanni bakwai da Najeriya ta buga ba a gasar cin kofin nahiyar Afirka ta AFCON na bana, inda kungiyar ta kare a matsayi na biyu.
Tsohon dan wasan gefe na CSKA Moscow ya fara buga wa tawagar kasar wasa a shekarar 2021 a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya da Cape Verde.
Ya buga minti 67 a ci 2-0.
Fitowar da ya yi a baya-bayan nan shi ne wasan da ya buga na mintuna bakwai a wasan sada zumunci da Guinea a watan Janairu.
Musa dai ya kasance ba shi da kulob tun bayan da aka soke kwantiraginsa da kungiyar Sivasspor ta Turkiyya a watan Fabrairu.
Amma da yake zantawa da manema labarai bayan wasan sada zumunta da ya shirya, Musa ya bayyana cewa: “Na dan tafi hutu ne kawai daga tawagar kasar.
“Amma ban fita daga tawagar ba.”


