An tabbatar da mutuwar mutum 19 a wani mummunan hadarin mota a da ya auku a kan hanyar Yangoji zuwa Gwagwalada a Abuja.
Da yake tabbatar wa da kamfanin dillacin labarai na NAN ya ce, adadin wadanda suka mutun, mai rikon kwaryar babban kwamandan hukumar Mr kiyaye hadura ta kasa Mista Dauda Biu, ya ce, hatsarin ya rutsa ne da motoci uku.
Ya kara da cewa hatsarin ya rutsa da mutum 31, inda mutum takwas suka samu munanan raunuka, yayin da kuma 19 suka mutu.
Ya ce bincike ya nuna cewa gudun wuce-kima tare da neman wuce juna ne ya haddasa aukuwar hatsarin.
Ana dai yawan fuskantar hadaran mota a manyan titunan Najeriya, wanda ake dora alhakin hakan kan rashin kyawun tituna, da tukin ganganci da uwa uba gudun da ya wuce kima da masu ababen hawa ke yi


