Akalla fasinjoji 20 ne suka kone kurmus a ranar Juma’a, a wani hatsarin da ya afku a mahadar Maya da Lanlate da ke karamar hukumar Ibarapa ta Gabas a jihar Oyo.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya tattaro cewa lamarin ya hada da wata motar bas ta kasuwanci da wata mota kirar Sienna.
NAN ta kuma tattaro cewa motocin guda biyu na tafiya ne ta gaba da gaba, inda suka yi karo da juna, inda motocin suka kama wuta nan take.
Wani ganau ya ce fasinjoji 20 da lamarin ya rutsa da su sun kone ba za a iya gane su ba.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, shugaban karamar hukumar Ibarapa ta Gabas Gbenga Obalowo, ya ce shi ne ya jagoranci tawagar ceto zuwa inda hatsarin ya afku.


