Adadin mutanen da suka mutu a harin da aka kai wani gidan rawa a Rasha a daren jiya ya kai 115 kamar yadda hukumar bincike ta ƙasar ta bayyana.
Kamar yadda ta bayyana a wani sakon manhajar Telegram da ta aika, tawagar da take lura da lamarin ta ce, masu aikin agajin gaggawa da ke duba ɓaraguzan ginin sun sake gano gawarwaki da dama yayin aikinsu a zauren.
“Adadin a yanzu ya haura 115,” tana cewa kuma har yanzu ana ci gaba da bincike. In ji BBC.


