Dakta Ahmed Abubakar Audi, Kwamandan Rundunar Tsaro ta Civil Defence (NSCDC), ya ce an lalata matatun mai ba bisa ka’ida ba 50, an kwato manyan motoci 300 tare da kama mutane 200 da ake zargi a cikin shekara guda.
Da yake magana a Abuja ranar Juma’a a yayin wani taron dabarun yaki da kwamanda da shugabannin rundunonin yaki da barna a kasar, ya bayyana aniyar hukumar ta NSCDC na sauya yanayin da ake ciki a kowane bangare na kasar.
A cewar sa, “Satar man fetur da barasa ba bisa ka’ida ba na karuwa, amma muna kan haka; don haka ne muka tsara taron don samar da mafita kan wannan matsalar.”
Babban Kwamandan ya bayyana cewa hukumar ta fara bincike na gaskiya a kan ayyukan jami’an da ke yaki da barna a fadin Jihohin kasar, da nufin dakile duk wasu bata-gari a kasar nan.


