Kungiyar ‘yan kasuwan kasar China a Najeriya CBCAN, ta mayar da martani kan kisan da aka yi wa Ummukulsum Buhari a Kano.
Matar mai suna Ummita, an zargi wani dan kasar China Geng Quanrong ne ya kash tai a daren Juma’a.
Wata sanarwa da shugaban CBCAN, Mike Zhang ya fitar a ranar Litinin ya yi Allah wadai da wannan mummunan kisan.
Zhang ya ce kamata ya yi a bar hukumomin tsaro da abin ya shafa su kula da wannan aika-aika cikin kwarewa.
“Al’ummar Sinawa a Kano suna goyon bayan dokar da ta dace,” in ji shi.
Ya ce jama’ar kasar Sin sun yaba da karramawar da aka yi musu a Kano kawo yanzu, kuma za su ci gaba da bin doka da oda, da ba da gudummawa ga ci gaban jihar.
Sanarwar ta kuma jajantawa iyalan mamacin wanda ya kammala karatunsa na kimiyyar aikin gona a jami’ar Kampala.
Ummita mai shekaru 23 ta kasance mamba a hukumar yi wa kasa hidima (NYSC).


