Rahotanni daga Ethiopia na cewa ana ci gaba da yaƙi a yankin Amhara da ke arewacin ƙasar bayan rushe tsagaita wutar da aka yi na tsawon wata biyar a makon jiya.
Mayaƙan Tigray sun ƙwace iko da garin Kobo da ke yankin Amhara bayan da suka nausa Kudancin ƙasar kusa da kan iyaka.
Mazauna garuruwa da ƙauyuka da suka tattauna da BBC sun ce an ci gaba da faɗa a cikin tsaunukan da ke kusa dasu kuma kamar baza a daina ba.
A halin yanzu hukumomi a Woldia da Dessie- manyan garuruwan Amhara biyu da ke kusa da yankin sun ƙaƙaba taƙaitacciyar dokar hana fita da daddare.
Gwamnatocin Oromia da yankin Somali da ke gabashi sun bayyana goyon bayansu ga sojoji da yankunan Amhara da na Afar da ke fuskantar sabbin hare-hare.
A lokacin da ake ganiyar yaƙi a bara, yankuna da dama sun aika sojoji zuwa filin daga.
Akwai zarge-zarge da ake yaɗawa a shafukan sada zumunta cewa faɗa na iya dawowa kan iyakokin Tigray da Eritrea mai maƙwabtaka.
Babban jami’in Tigray Getachew Reda ya yi ikirarin cewa jami’an rundunar sojin Habasha sun tsallaka kan iyakoki domin haɗa kai da Eritrea.
Zuwa yanzu dai BBC bata tabbatar da wannan ikirari ba.
Firamnista Abiy Ahmed wanda har yanzu bai fito fili ya yi magana ba tun bayan dawowar yaƙin, ya kai wata ziyarar aiki zuwa Algeria.


