Wata mata a jihar Madhya Pradesh da ke kasar India ta samu munanan raunuka sakamakon fadan da ta yi da wata damisa domin kubutar da danta mai shekara daya da wata uku.
Matar, mai suna Archana Choudhary, ta kwashe mintuna masu yawa tana kokawa da damisar, kafin mazauna kauyen Bandhavgarh su jiyo ihunta, su kawo mata dauki.
Yanzu haka dai uwar tare da yaron nata na kwance a asibiti inda ake yi musu magani.
Dabbobi a Indiya dai na yawan farmakar jama’ar da ke zaune a kusa da gandun dajinsu.
Wani mazaunin kauye a kasar ya shaida wa BBC cewa baya ga damisa, a mafiya yawan lokuta giwaye kan shiga gonakinsu, su kuma lalata musu amfanin gona.


