Masanin siyasa, Farfesa Kamilu Sani Fagge, ya ce, Bola Tinubu zai iya fuskantar kalubale a 2023 a wajen gwamnonin jam’iyyar APC.
Cikin zantawarsa da BBC ya ce, ”Wasu daga cikinsu na neman samun kujerar mataimakin shugaban ƙasa, wasu shugabancin jam’iyya wasu kuma kujerar shugaban ƙasar ma suke nema, kuma suna ganin cewa sanya Tinubu a gaba zai iya daƙile cikar nasu burinsu” in ji shi.
Dakta Abubakar Kari kuwa cewa, ya yi wasu daga cikin waɗannan gwamnoni da ke fatan zama mataimakin shugaban ƙasa na ganin cewa idan Tinubu zai yi wa APC takara to yawancinsu ba zai yiwu su samu wannan kujera ba, domin a matsayinsa na Musulmi ana sa ran zai ɗauko Kirista ne domin yi masa mataimaki, don haka tunda su musulmai ne zai yi wuya su samu wannan dama, saboda zai yi wuya a haɗa musulmi da musulmi su yi takara.
“Ko a yankinsa na kudu maso yamma ma ba za ka iya cewa dukkan gwamnonin na goyon bayansa ba, biyu daga ciki ne za ka iya cewa suna goyon bayansa, gwamnan Osun wanda ɗan uwansa ne, da kuma gwamnan Legas wanda shi ya kawo shi,” a cewar Dakta Kari.
Kazalika Dakta Kari ya kara da cewa mataimakin shugaban Farfesa Yemi Osinbajo zai iya zame wa Tinubu ƙashin-wuya, domin a fili take cewa akwai wasu makusantan Shugaba Muhammadu Buhari waɗanda ba sa son Tinubo, don haka abu ne mai wuya su amince da shi.
”Wasu na ganin cewa sai lallai kana da tsari, sannan ka kafu a siyasance za ka iya zama shugaban ƙasa, amma a zahiri mun san cewa ko Jonathan lokacin da ya zama shugaban ƙasa ba shi da wani tsari na siyasa, sannan bai yi kafuwar da za ka ce ita ce ta sa ya ci zaɓe ba, don haka babu abun da zai sa hakan ya yi tasiri a kan Osinbajo a yanzu” a cewar Kari.