Manyan mutane 500 ciki har da shugabannin kasashe da firaiministoci da kuma sarakuna a fadin duniya ne suka halarci addu’ar da aka yi wa Sarauniya a majami’ar Westminister Abbey
Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai shugaba Biden da mai dakin shugaban Ukraine Olena Zelenska da shugabannin Jamus da Faransa da Afirka ta Kudu da India da kuma mataimakin shugaban China.
Kasashe kalilan ne aka cire su daga zuwa jana’izar ciki har da Rasha da kuma Belarus, saboda yakin da ake yi a Ukraine. Syria da Myanmar da Afghnaistan da kuma Venezuela ma ba su halarci taron ba


