Ma’aikatar kudi da kasafi da tsare-tsare ta bayyana cewa majalisun tarayya da na jihohi da kuma kananan hukumomi sun raba Naira biliyan 675.946 daga asusun tarayya na watan Nuwamba a ranar Juma’a.
Olajide Oshundun, mukaddashin daraktan yada labarai na ma’aikatar kudi, kasafin kudi da tsare-tsare ta kasa ne ya bayyan hakan ranar Asabar a Abuja.
Gwamnatin tarayya ta karbi Naira biliyan 261.441 na kudaden, yayin da jihohi da kananan hukumomi suka samu Naira biliyan 210.046 da kuma Naira biliyan 155.456.
Jihohin da su ke hako mai sun samu karin Naira biliyan 49.003 a matsayin kashi 13 na asusun rarar man.
Jimlar kudaden shiga na VAT da a ka tara a watan Nuwamba ya kai Naira biliyan 196.175 sabanin Naira biliyan 166.284 a watan Oktoba, wanda ya nuna an samu karin Naira biliyan 29.891.
Daga kudaden shiga na VAT, gwamnatin tarayya ta samu Naira biliyan 27.402, yayin da jihohi da kananan hukumomi suka samu Naira biliyan 91.339, da kuma Naira biliyan 63.937.
Hukumar tara kudaden shiga ta tarayya da hukumar kwastam ta Najeriya da hukumar kula da harkokin man fetur ta Najeriya ta samu Naira biliyan 7.847 a matsayin kudin tattara kudaden shiga yayin da aikin hukumar raya yankin arewa maso gabas ya samu Naira biliyan 5.650.
Oshundun ya bayyana cewar, rabon kudaden shigar an gudanar da shi ne a wani a taron kwamitin raba asusun ajiya na tarayya wanda babban sakatare a ma’aikatar Mista Aliyu Ahmed ya jagoranta.