A yau ne Majalisar Dokokin Jihar Ribas karkashin jagorancin Martins Amaewhule za ta sake tantancewa tare da tabbatar da sunayen kwamishinoni tara.
Kwamishinonin dai su ne wadanda suka yi murabus daga nadin nasu sakamakon zazzafar rikicin siyasar jihar tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike da kuma wani sashe na Majalisar karkashin jagorancin Amaewhule.
An yi imanin matakin da Majalisar ta dauka ya yi daidai da kudurori guda takwas da Fubara, Wike, da wasu manyan shugabanni suka rattabawa hannu kan rikicin siyasar jihar, bayan shiga tsakani na Shugaba Bola Tinubu.
Wani bangare na kudurin shi ne cewa a sake nada kwamishinonin da suka yi mulki.
Sai dai babu tabbas ko sunayen kwamishinonin gwamnan ne ya aika majalisar domin tantancewa da tabbatarwa ko kuma ‘yan majalisar na yin nasu ne.
A halin da ake ciki, Gwamna Fubara a jiya ya rantsar da sabbin Sakatarorin Dindindin 16 don gudanar da ayyukan gudanarwa na ma’aikatun, “har sai lokacin da ma’aikatun za su sami shugaban siyasa.”
Gwamnan ya kuma bayyana cewa nadin nasu ba siyasa bace.


