Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta yi alkawarin tabbatar da kare kuri’un da ‘yan Najeriya suka kada a zabukan da ke tafe, inda ta ce zamanin magudin zabe ya wuce.
Shugaban hukumar ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya yi wannan alkawarin ne a ranar Juma’a a lokacin da yake gabatar da jawabi a taron kaddamar da rahoton Yiaga Africa Election Analysis Dashboard, ERAD, Report on Electronic Transmission of Results a zaben Ekiti da Osun na 2022 a Abuja.
Mahmood ya ce INEC ta yi aiki tukuru don inganta gaskiya da kuma kara kwarin gwiwar ‘yan Najeriya kan yadda ake gudanar da sakamakon zaben.
“Zan iya da karfin gwiwa cewa kwanakin magudin zabe ba bisa ka’ida ba sun kare a fili.
“Duk da haka, ba mu tsaya kan bakanmu ba, sanin cewa dole ne mu ci gaba da yin matakai da dama a gaban masu neman kawo cikas ga tsarin kuma akwai miyagu da dama a fagen kokarin kawo cikas ga tsarin, amma mun tsaya ne da adalci a zabe.
“Za mu tabbatar da cewa an kare kuri’un da ‘yan Najeriya suka kada kuma shi ne kadai wanda zai tabbatar da wanda zai zama me a dimokuradiyyarmu,” in ji shi.
Ya kara da cewa adadin ma’aikatan wucin gadi da hukumar za ta tura domin gudanar da zaben 2023 ya zarce yawan jami’an ‘yan sanda da na sojoji.


