Gwamnatin jihar Legas ta dakatar da ayyukan kungiyar sufuri a jihar Legas, biyo bayan barazanar da shugaban kungiyar NURTW ya yi na cewa za a iya dakatar da reshen kungiyar a Legas.
Yankunan da lamarin ya shafa sun hada da titin Church da Eyin Eyo da gadar Idumota, sakamakon rikicin baya-bayan nan da ya gurgunta al’amura a yankin Idumota na jihar.