Rahotanni sun tabbatar da cewa, Malamin da ake zargi da ya kashe Hanifa a jihar Kano, ya kai ziyarar jaje tare da gursheken kuka a lokacin da ake zaman jimamen neman marigayiya Hanifa.
Rahotanni sun tabbatar da cewa, Malamin ya je gidan su Hanifa tare da jajanta musu tun a lokacin da ake neman Hanifa.
Tun bayan faruwar lamarin tuni dai mutane a shafukan su na sada zumunta ke ta dora hoton Hanifa tare da yin Allah wadai da wannan batun.