A yau ne iyalan tsohon firaministan Burtaniya Boris Johnson ke tattara komatsansu a shirye-shiryen da suke yi na bankwana da gidan firaministan wanda ke Downing Street, domin bayar da waje ga sabuwar firaministar Mrs Liz Truss tare da iyalanta, wacce za ta ci gaba da zama a gidan na tsawon mulkinta,
To sai dai yayin da ake wannan shiri na ficewa daga gidan Kyanwar gidan mai suna ‘Lary’ na nan daram a gidan tana jiran isowar sabuwar firaministar
Lary wacce ba mallakin kowa ba ce, ta zama babbar Kyanwar gidan firaminstan Burtaniya.
Kyanwar mai shekara 15, wacce ta yi zamani da firaministocin Burtaniya har guda uku, na shirin zama da iyalan Mrs Truss. A cewar BBC.


