Wata kotun majistare da ke zamanta a Ajah a jihar Legas, ta bayar da umarnin tsare mawakai, Panshak Zamani, wanda aka fi sani da Ice Prince, a ci gaba da tsare shi a gidan yari na Ikoyi bisa zarginsa da cin zarafin wani dan sanda.
Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta gurfanar da Ice Prince a gaban kotu a ranar Juma’a, bisa tuhume-tuhume uku da suka hada da cin zarafi, dakile da kuma sace wani dan sanda.
Ya ki amsa laifin da ake tuhumarsa da shi lokacin da aka karanta masa.
Alkalin kotun mai shari’a Taiwo Oyaniyi ya bayar da belinsa a kan kudi Naira dubu 500,000. Ya kuma bada masu tsaya masa guda biyu.
Ya ci gaba da zama a gidan yarin Ikoyi har zuwa cika sharuddan belinsa.
An kama mawakin ne da sanyin safiyar Juma’a, kamar yadda kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Legas, Benjamin Hundeyin ya bayyana.
Ya ce an tsayar da mawakin ne saboda tukin mota ba tare da tambarin mota ba, amma ana zargin ya yi awon gaba da dan sandan ne a cikin motarsa tare da cin zarafin dan sandan.
Hundeyin a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Juma’a, ya kuma yi zargin cewa mawakin ya yi barazanar jefa jami’in a cikin kogi.
“Da karfe 3 na safiyar yau, an dakatar da @Iceprincezamani saboda tukin mota ba tare da tambarin mota ba. Ya amince a kai shi tashar.
“Bayan haka, ya yi awon gaba da dan sandan a cikin motarsa, ya afka masa tare da yi masa barazanar jefa shi a cikin kogin. An kama shi kuma za a gurfanar da shi a yau,” Hundeyin ya wallafa a shafinsa na Twitter.
Damuwa Yayin Da FG Ta Kai Masu Kudaden Ta’addanci Kotu


