fidelitybank

Kotu ce ƙadai za ta iya sakin Nmandi Kanu – Buhari

Date:

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya tabbata da cewa, kotu ce kaɗai za ta iya sakin shugaban ƙungiyar IPOB, Nmandi Kanu.

‘Yan makonni bayan alƙawarin da ya yi wa dattawan al’ummar Ibo na duba yiwuwar sakin ɗan tawaye, Nnamdi Kanu, Buhari ya ce “ba za mu iya sakin sa ba”.

Ya ce: “Akwai sashen da ba zan iya taɓawa ba, shi ne na shari’a. Batun Kanu ya na gaban kotu. Amma abin mamakin shi ne, lokacin da ya ke Turai ya na zagin wannan gwamnati, na zaci zai so ya zo ya kare kansa daga waɗan nan zarge-zargen.

“Saboda haka muna ba shi dama ce ta kare kan sa bisa tsarinmu, ba wai ya koma Turai ya ci gaba da zaginmu ba kamar ba ɗan Najeriya ba. Ya zo nan ya soke mu…waɗanda ke cewa ya kamata a sake shi, a’a, ba zamu iya sakin sa ba.”

A watan Nuwamba ne dattawan suka gana da Buhari a Abuja, inda suka nemi ya tausaya wa jagoran na haramtacciyar ƙungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB) da ke neman kafa ƙasar Biafra a kudu maso gabashin Najeriya.

Buhari na wannan jawabin ne yayin tattaunawar sa da gidan talabijin na Channels.

sun news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

JAMB ta amince da maki 150 mafi ƙanƙanta don samun gurbin karatu a jami’o’i

Hukumar shirya jarrabawar shiga Jami'o'i ta Najeriya (JAMB) ta...

ASUU ta dakatar da yajin aikin da ta fara

Ƙungiyar Malaman Jami'o'i ta Najeriya, ASUU da dakatar yajin...

Masu haɗakar ADC na ɓaɓatu ne saboda rashin gwamnati – Radda

Gwamnan jihar Katsina, Mallam Dikko Umar Radda ya yi...

Ba ruwan Biri da gada a makamin Nukiliya – Shettima

Mataimakin shugaba Najeriya Kashim Shettima ya ce ƙasar za...

An kashe Mutane 70 a jihar Filato

Rahotonni daga jihar Filato na cewa ƴanbindiga sun kai...

Ambaliya ta kashe mutane 100 a Amurka

Hukumomi a jihar Tesxas da ke Amurka sun bayyana...

Tsohon Ministan kuma jigo a PDP ya koma ADC

Tsohon ministan harkokin ‘yan sanda kuma sau uku a...

Trump ya caccaki Elon Musk

Shugaban Amurka Donald Trump ya caccaki tsohon mashawarcinsa, Elon...

Dalilin da ya sa Kwankwaso ya ki shiga jam’iyyar hadaka – Galadima

Jam'iyyar NNPP ta ce abin da ya sa ba...

Obi ba zai taba zama shugaban kasa ba – Wike

Ministan Abuja, Nyesom Wike ya ce, tsohon ɗan takarar...

Ƴansanda sun kama ƴan Ghana 19 da aka yi safararsu a Najeriya

Rundunar ƴansandan Najeriya ta kuɓutar da wasu ƴan Ghana...

Benue da Edo da Bayelsa na fargabar balewar madatsar ruwan Kamaru

Gwamnatocin jihohi uku na cikin shirin ko-ta -kwana, sakamakon...
X whatsapp