fidelitybank

Ko a biya ma’aikata albashin su a Zamfara ko mu tsunduma yajin aiki – Likitoci

Date:

Kungiyar likitocin Najeriya (NMA) reshen jihar Zamfara, ta bai wa gwamnatin jihar wa’adin mako guda ta biya ma’aikatan lafiya 17 albashinsu na wata hudu da sauran ma’aikatan lafiya a asibitin kwararru na Yarima Bakura ko kuma su shiga yajin aiki.

Shugaban NMA na jihar, Dakta Sanusi Bello, wanda ya yi wa manema labarai jawabi a ranar Litinin a Gusau, babban birnin jihar, ya kuma bayar da misali da albashin dukkan likitocin asibitin na watan Yuli 2023, da alawus na wata takwas ga kwararrun likitoci da ba a biya, wanda ya sa suka daina aiki.

Bello ya ce kungiyar ta yanke shawarar bayar da wa’adin mako guda ga gwamnatin jihar Zamfara domin ta magance wadannan bukatun.

Ya kara da cewa ƙungiyar a Zamfara za ta ci gaba da yajin aikin sai baba ta gani daga ranar Litinin 4 ga Satumba, 2023, idan har gwamnati ta kasa biya musu bukatunsu.

Shugaban ya yi gargadin cewa matakin zai kai ga rufe dukkanin asibitocin da suka hada da asibitocin gwamnatin tarayya da asibitocin jiha da asibitoci masu zaman kansu da kuma janye duk wani aikin lafiya da na hakori da duk likitocin jihar Zamfara ke yi.

assu news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp