Bualaliyar majalisar dattawa, Orji Uzor Kalu, ya bayyana jin dadinsa kan ziyarar da ya kai jihar Enugu a ranar Kirsimeti.
Tsohon gwamnan jihar Abia, a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Lahad, ya ce” Ziyarar da ya kai garin Kwal ta yi matukar ban mamaki”, inda ya ce”Gwamna Ifeanyi Ugwuanyi, babban kwamandan runduna ta 82 na sojojin Najeriya, Manjo Janar T.A Lagbaja ne ya tarbe shi.
Jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC), wanda ya raba wasu hotuna daga ziyarar, ya ce, “hakika bikin Kirsimeti a Enugu jiya ya yi matukar ban sha’awa domin na kasance bako ga wasu fitattun ‘yan kasa guda hudu.
”Abokina kuma Gwamnan Jihar Enugu, Rt.Hon Ifeanyi Ugwuanyi ya karbe ni cikin nishadi. Abokina kuma tsohon Sakatare na dindindin, Sir Chinyeaka Ohaa ya karɓe ni. Babban kwamandan runduna ta 82 ta sojojin Najeriya, Manjo Janar T.A Lagbaja ne ya karbi bakwancin mu, kuma kungiyar OUK Movement reshen Enugu karkashin jagorancin, Hon Emeka Edeh, ita ma ta karbe mu da kuma nishadantar da mu. Na gode Enugu.” A cewar Orji.
PlatinumPost ta rawaito cewa, Kalu ya yi shiru a kan sha’awarsa tsayawa takara a zaben shugaban kasa na 2023 a karkashin jam’iyyar APC a daidai lokacin da a ke ta cece-kuce kan cewa yankin Kudu maso Gabas ya kamata ya samar da Shugaban kasa.