Majalisar dokokin jihar Kano, ta kafa kwamitocin wucen gadi har guda 6, wadanda za su yi aikin kare kasafin kudin baɗi na ƙananan hukumomi 44 na jihar Kano.
Kwamishinan ƙanan hukumomi, Alhaji Murtala Sule Garo ne ya aikewa da majalisar mai ƙunshe da kasafin wanda shugaban majalisar, Injiniya Hamisu Ibrahim Chidari, ya karanta a zauren majalisar na ranar Laraba.
Injiya Ibrahim Chidari, kuma ce kwamitocin za su gudanar da ayyukan su.
A lokacin zaman majalisar, gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi masu jiragen ruwa da su guji ɗaukar mutanen wuce ƙima domin magance matsalar mutuwar mutane a jihar, yayin da mai wakiltar Bagwai da Shanono, Alhaji Isah Ibrahim Ali Shanono ya miƙa saƙon godiya ga mutanen da su ka tallafa da haɗarin ƙwale-ƙwale a yankin su.