Mai martaba sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya nada Alhaji Tajuddeen Bashir Baba a matsayin sabon mai unguwar Yakasai.
Nadin ya biyo bayan mutuwar tsohon mai unguwar Yakasai, Bashir Baba, wanda mahaifi ne ga sabon mai unguwar ta Yakasai.
Aminu Ado Bayero ya ce, sun ba shi wannan matsayin ne bisa irin jajircewarsa da mahaifinshi ya ke wajen samar da tsaro a yankunan Yakasai.
A nasa jawabin sabon mai unguwar, Alhaji Tajuddeen Bashir Baba, ya yi godiya ga al’ummar Yakasai da su ka zabe shi a matsayin mai unguwar Yakasai, kuma zai daura daga inda mahaifinsa ya tsaya.