Rundunar sojin ruwa ta Amurka ta bayyana cewa jiragen ruwanta biyu na yaƙi za su wuce ta mashigin ruwa Taiwan.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da China ke gudanar da wani babban atisaye ta wurin domin nuna ɓacin ranta, kan ziyarar da shugabar majalisar tarayyar Amurka Nancy Pelosi ta kai Taiwan ɗin a kwanakin baya.
Amurka ta ce jiragen ruwan biyu na wucewa ne ta wurin sakamakon ƴancin da suke da shi na kutsawa cikin teku a fadin duniya.
A ƴan shekarun nan, sojojin ruwa na Amurka da na wasu ƙasashen yamma sun mayar da mashigin ruwan na Taiwan a matsayin wani wurin yada zango.
Sai dai China na ɗaukar hakan a matsayin tsokanar faɗa inda har yanzu take kallon Taiwan ɗin a matsayin ɗaya daga cikin yankunan ƙasarta. In ji BBC.


