Jakadan Najeriya a kasar Spaniya, Demola Seriki ya rasu ya na da shekara 63 a duniya.
Wata sanarwa da iyalansa suka fitar ta ce jakadan kuma tsohon minista ya rasu ne a yau Alhamis.
A watan Janairun 2021 ne Shugaba Muhammadu Buhari ya nada shi a matsayin jakadan Najeriya a Spaniya.
Kafin wannan mukamin, ya taba rike mukamin karamin minista a ma’aikatar tsaro da kuma na aikin gona.