Gwamnan jihar Imo, Sanata Hope Uzodinma, ya bayyana cewa, ‘yan kabilar Igbo sun gina Fatakwal, babban birnin jihar Ribas.
Gwamnan ya yi wannan ikirarin ne a yayin bikin zagayowar ranar haihuwar wani dattijon dan jihar Imo, Emmanuel Iwuanyanwu, a Owerri, babban birnin jihar Imo a bikin cikarsa shekaru 80 da haihuwa.
Gwamna Uzodinma ya kara da cewa wasu mutane na kokarin sake rubuta tarihi.
A cewarsa, “’yan kabilar Igbo ne suka gina Fatakwal. Ko da ya faranta wa wasu rai a yanzu don ƙoƙarin sake rubuta tarihi.
“Ibo ne suka gina Fatakwal.”
Gwamnan ya ci gaba da cewa ‘yan kabilar Igbo na matukar kaunar Najeriya, kamar yadda ake samun su a kowane bangare na kasar nan.
“Shahararrun ‘yan kabilar Igbo irin su marigayi Dokta Nnamdi Azikwe, Ikemba Odumegwu Ojukwu, har da Janar Ike Nwachukwu da sauran manyan mutane maza da mata, iyayensu ne suka haifa a Arewa a matsayin gidansu.
“Hakika, a fadin kananan hukumomi 774 na Nijeriya, daga Zungeru a Arewa zuwa Owo a Yamma da kuma daga Akwanga zuwa Ahoada, ana samun ‘yan kabilar Igbo da yawa a wurin.
Ya kara da cewa “A mafi yawan lokuta, a wajen ‘yan asalin kasar, mafi yawan kabilun da ke wajen kasar Igbo su ne Igbo.”


