Daya daga cikin jiga-jigen da su ka kafa jam’iyyar APC tare da kasancewa na gaba-gaba wajen fafutukar ganin shugaba Muhammadu Buhari ya samu mulkin Najeriya, Injiniya Buba Galadima, ya ce bai gamsu da kamun ludayin gwamnatin Buhari ba.
A hirarsa da BBC ta yi da Buba Galadima, ya ce, a yanayin salon jagorancin jam’iyyar da kuma mulkin da a ke yi a kasar a yanzu, lamarin ya ba su mamaki, domin sun yi zaton za a samu gagarumin sauyi a kasar zuwa yanzu, amma hakan ba ta kasance ba.
Ya ce”Abin takaicin shi ne Allah ya jarrabi shugaba Muhamadu Buhari da rashin lafiya, kuma dadin dadawa sai jam’iyyar ta kasa samar da wani kyakkyawan shugabanci, wanda duka wadannan abubuwa sun shafi yanayin mulkin”. Inji Buba Galadima
Game da rashin ba shi wani mukami ko tafiya da shi a gwamnatin Buharin, Buba Galadima ya musanta cewa akwai wani sabani a tsakaninsu da Shugaban, wanda ake rade-radin cewa, saboda hakan ne ba a tafiyar da shi.