Sashen leken asiri na rundunar hadin guiwa ta rundunar soja a yankin arewa maso gabas, Operation Hadinkai, Kanal Obinna Ezuipke, ya bayyana cewa, 98 daga cikin 276 ‘yan matan da ‘yan ta’addan Boko Haram suka sace a makarantar sakandaren ‘yan mata ta gwamnati da ke garin Chibok a jihar Borno a ranar 14 ga Afrilu, 2014. har yanzu suna cikin zaman talala.
Shugaban sashen leken asiri na rundunar hadin guiwa ta rundunar soji a shiyyar Arewa maso Gabas ta Operation Hadinkai, ya bayyana hakan ga manema labarai a hedikwatarsu da ke Maimalari Cantonment a Maiduguri ranar Asabar.
Ya bayyana cewa daga cikin ‘yan matan Chibok 276 da aka sace, ‘yan mata 57 ne suka tsere a shekarar 2014 yayin da aka sako ‘yan mata 107 a shekarar 2018.
Shugaban sashen leken asirin ya kara da cewa an ceto ‘yan mata uku a shekarar 2019, biyu a shekarar 2021 da kuma 9 a shekarar 2022, wanda adadinsu ya kai 178.


